SUBHANALLA: Kalli Yadda Ake Kekketa Kur’ani Ana Cusawa A Cikin Wani sabon Gida da ake Ginawa A Kano
A jihar Kano al’umma sun gano wani gida da ake ginawa a Unguwar Damfami ta yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, wanda ake zargin ana cusa takardaun Al-Qur’ani da Alluna da rubutu ana gine su a ginin gidan.
Kazalika, Al’ummar wannan yankin, sun yi ƙorafi kan ba za su bari a ci gaba da irin wannan ginin a cikin yankin su, Hakan tasa tuni suka rushe ginin tare da miƙa mai gidan hannun hukuma.
Sannan a fili din gidan sai akai amfani da Alluna wajen zuba lintar gidan kamar yadda gidan radio Dala FM kano ya rawaito.
Al’ummar wannan yanki sunyi kira ga hukumar hisbah da tazo ta dauki mataki tunkan yan unguwa su dauki doka a hannu.
Allah Ta’ala mun tuba ka yafe mana karka kama mu da laifin wasu daga cikin wawayen cikin mu.
Gadai videon a kasa
0 Response to "SUBHANALLA: Kalli Yadda Ake Kekketa Kur’ani Ana Cusawa A Cikin Wani sabon Gida da ake Ginawa A Kano"
Post a Comment