--
Yanzu yanzu: Ansaki Hotunan 'Yan Boko Haram din da suka tsere daga Gidan yarin Kuje

Yanzu yanzu: Ansaki Hotunan 'Yan Boko Haram din da suka tsere daga Gidan yarin Kuje


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sunayen wadanda suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata.


Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ce ta fitar da jerin sunayen na mutum 69 a ranar Juma'a, kwana uku bayan kai harin.


A sakon da ta aika wa manema labarai, hukumar gidan yarin ta wallafa har da hotunan mutanen.


Hukumar gidan yarin ta ce za a iya kallon cikakken jerin sunayen a shafinta na intanet www.corrections.gov.ng


A jikin hotunan mutanen da aka wallafa din duk suna sanye da inifom din gidan yarin, kuma da sunan kowa a kasan hoton.


Hoton mutum 69 ne hukumar gidan yarin ta fitar, wadanda ta ce na 'yan kungiyar boko haram ne da wasu daurarru wadanda shari'arsu take da nasaba da ta'addanci, wadanda suka arce daga gidan kurkukun bayan 'yan bindiga sun fasa gidan.


Hukumar ta jera hutunan wadanda suka tseren ne da sunayensu. Kana ta ba da wasu lambobin waya da ta ce 'yan Najeriyar za su iya tuntubarta ta layukan wayan, don sanar da jami'anta duk wani bayanin da zai taimaka wajen cafke su.


Sai dai da wuya mutane su rarrabe wadanda ake zargi da ta'addancin ta sunayen da aka wallafa, kasancewar sunaye ne na yanka.


Alhali mafi yawan mayakan boko haram sun fi shahara ne da lakabi…inda, misali  za ka ji ana ce da su Abu wane da makamantansu.


Sannan an wallafa sunan garuruwansu da yarensu da kuma adireshinsu.


Kazalika hukumar gidan yarin ta ce za ta fitar da karin bayani a kan sauran daurarrun da suka gudu daga kurkukun Kujen.










0 Response to "Yanzu yanzu: Ansaki Hotunan 'Yan Boko Haram din da suka tsere daga Gidan yarin Kuje"

Post a Comment