--
Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu

Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu


Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu.


Tsula-tsulan 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa Yaradua sun haskaka wurin shagalin auren Shehu Yaradua da Yacine Sheriff A hotunan da aka tattaro, an ga matan tsofaffin gwamnoni, Zainab Dakingari da Nafisa Shehu Shema suna walkiya tamkar taurari a wurin taron bikin, 


Hajiya Turai Yaradua ma bata yadda makaman gayunta ba, ta bayyana cike da ado inda take nuna farin cikin ranar tare da jikokin marigayin shugaban kasan 


Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Umaru Musa Yar'adu a wurin shagalin auren Shehu Yaradua sun bayyana. 


A hotuna da bidiyoyin da aka tattaro da @weddingstreet_ng a Instagram, 'yan uwan angon sun fito shar da su a wurin shagalin auren 'dan uwansu inda suka dinga haskawa tare da walkiya. 


Iyalan marigayin tsohon shugaban kasan sun hada da matan tsofaffin gwamnonin Najeriya irinsu Nafisa Shehu Shema, Zainab DakinGari da sauransu. 


Sun caba ado iyakar kure adaka inda suka saka kaya na alfarma masu matukar birgewa da jan hankali, inda masu kwalliyar zamani suka caba musu kwalliyar kece raini. 


Hajiya Turai Yaradua ma ba a bar ta a baya ba, ta caba adonta inda ta fito shar. Ta bayyana a wasu hotuna da ta dauka da 'ya'yanta tare da jikokinta duk a yayin shagalin taya Shehu Yaradua angwancewa. 

0 Response to "Kyawawan hotuna da bidiyoyin 'ya'ya da jikokin marigayi shugaba Umaru Musa 'Yaradua a wurin bikin 'dan uwansu"

Post a Comment