Matashi ya buga Wasan Bet9ja da N800 kuma ya ci Naira miliyan N38,317,130 (Kalli Video)
Wani dan Najeriya ya zama hamshakin attajirin dare daya bayan ya yi nasara sosai ta hanyar cacar wasanni. wadda akafi sani da { Betnaija}
An ce yaron da ya yi sa’ar ya yi amfani da Naira 800 wajen buga wasan Bet9ja kuma ya samu zunzurutun kudi har Naira miliyan 38 (Naira Miliyan Talatin da Takwas).
Bidiyon da aka yada ya nuna lokacin da jama'a suka taru a cibiyar Buga wasannin ta {Betnaija}| don tabbatar da labarin.
Da aka duba allo a cibiyar, ya nuna cewa mutumin, wanda har yanzu ba a tantance ba, ya samu jimillar N38,317,130.
Har ila yau, taron wanda ya kunshi 'yan mata da yawa sun bi sabon attajirin a lokacin da ya je Masallacin domin yin Sallah.
Ana jiyo su ana ta yabonsa yana alwala ya maida hankalinsa kan sallah, ba tare da la'akari da cewa duk sun zuba masa ba.
Kalli bidiyon a kasa:
KALLI BIDIYON ANAN LATSA YANZU
N800 to win N38m on Bet9ja & the whole streets followed him to Mosque. Wow. 👍pic.twitter.com/TpKqYS9sIt
— POOJA!!! (@PoojaMedia) October 18, 2022
0 Response to "Matashi ya buga Wasan Bet9ja da N800 kuma ya ci Naira miliyan N38,317,130 (Kalli Video)"
Post a Comment