--
An Buɗe Shafin Bayarda Tallafin Kuɗi Domin Ƙarfafa Ɗalibai ƴan Kasuwa Karkashin Shirin "GABI Studentpreneur Awards"

An Buɗe Shafin Bayarda Tallafin Kuɗi Domin Ƙarfafa Ɗalibai ƴan Kasuwa Karkashin Shirin "GABI Studentpreneur Awards"


GABI Studentpreneur Awards tallafi ne da ake bawa daliban Najeriya musamman wadanda ke karatu a University ko Polytechnic ko College ta Education domin domin habaka kasuwanci su da kuma samun ilimi na kasuwancin zamani shidai wannan tallafin ya kasu kashi biyu kashi na daya 


"THE TOP 3 STUDENTPRENUERS" da kashi na biyu "THE TOP 47 STUDENTPRENEURS" ina kira ga ɗalibai da su daure su cike kuma suyiwa yan uwansu ɗalibai sharing domin cin gajiyar sharin na GABI Studentpreneur Awards.


Cancanta


Dole ne mai cikewa ya kasance dan Najeriya

Dole ne ya kasance ɗalibi dake karatu a University ko Polytechnic ko College ta Education

Dole ne ɗalibi ya kasance mai kasuwanci ko shawar kasuwanci

Dole ne ya kasance mai dandalin Kasuwanci a shafukan sada zumunta musamman "Instagram"

Tsarin Bayarda Tallafi


Uku na farko daga cikin taurari za'a basu Naira Dubu Dari Biyar (N500,000)

Mutum Hamsin 50 na farko za'a basu horon kasuwanci na watanni uku 3

Za'a Tallata masu hajarsu na tsawon watanni uku 3

Za'a kuma dora su kan Business Networking.

Yadda Zaku Cike


Domin cin gajiyar tallafin GABI Studentpreneur Awards ku ziyarci shafin yanar gizo-gizo da ke a kasa


Samu Karin Bayani: https://gabimag.com/spa/

Cikewa Kai Tsaye: https://gabimag.com/spa-entry/

ALLAH Yasa Mu Dace Baki Daya kuma yasa mu cike cikin nasara


0 Response to "An Buɗe Shafin Bayarda Tallafin Kuɗi Domin Ƙarfafa Ɗalibai ƴan Kasuwa Karkashin Shirin "GABI Studentpreneur Awards""

Post a Comment