--
 Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alla-wadai Da Alkawarin Da Atiku Ya Yi Na Buɗe Bodoji Idan Ya Ci Zaɓe

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alla-wadai Da Alkawarin Da Atiku Ya Yi Na Buɗe Bodoji Idan Ya Ci Zaɓe

👇👇👇👇👇👇👇

https://youtu.be/o0vlDmBJVa4 


Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alla-wadai Da Alkawarin Da Atiku Ya Yi Na Buɗe Bodoji Idan Ya Ci Zaɓe. 


Gwamnatin tarayya ta bayyana, a matsayin abin takaici, alkawarin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dauka na sake bude iyakokin Nijeriya idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya yi wannan alkawarin ne a yayin gangamin yakin neman zabensa a Katsina a ranar Talata.


Sai dai ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce Atiku a cikin fafutukar sa ta neman mulki, na neman dawo da Nijeriya zamanin shigowar makamai ba tare da kakkautawa ba tare da shigo da abinci da yawa don cutar da manoman gida.


Ministan ya yi wannan jawabi ne a jiya Alhamis a Abuja a wajen taron bita kan ayyukan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, PMB, karo na 15.


A cewar ministar, alkawarin da Atiku ya yi, idan har ya aiwatar da shi, zai jefa miliyoyin ƴan Nijeriya cikin halin rashin aikin yi tare da lalata kamfanonin takin zamani da na shinkafa da su ka yi yawa tun bayan da Nijeriya ta rufe iyakokinta a shekarar 2019.


Ya kara da cewa manufar da Atiku ya tsara zai kara tabarbare harkokin tsaro a Nijeriya ta hanyar sanya dukkani kan iyakokin kasar su zama wara-wara da ba da damar shigowa da makamai cikin kasar nan. 


Mohammed ya ce a cikin sanarwar, Atiku ya sanar da ‘yan Najeriya cewa zai yi watsi da duk kokarin da gwamnatin Buhari ta yi na samun dogaro da kai wajen samar da kayan abinci da dama musamman shinkafa.


Ya kara da cewa miliyoyin manoman shinkafa za su rasa ayyukan yi idan shinkafar da ake shigowa da ita daga kasashen waje ta mamaye kasar nan yayin da dubban daruruwan ‘yan Nijeriya da ke aiki a masana’antar shinkafa daban-daban da aka kafa karkashin gwamnatin Buhari su ma za su zama marasa aikin yi.

0 Response to " Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alla-wadai Da Alkawarin Da Atiku Ya Yi Na Buɗe Bodoji Idan Ya Ci Zaɓe"

Post a Comment