--
 Jami'an hukumar Hisbah sun cika hannu da wasu matasa 19 a kokarinsu na kulla auren jinsi daya

Jami'an hukumar Hisbah sun cika hannu da wasu matasa 19 a kokarinsu na kulla auren jinsi daya

 



Jami'an hukumar Hisbah sun cika hannu da wasu matasa 19 a kokarinsu na kulla auren jinsi daya


 Yan Hisbah sun kama mata 15 da maza hudu a wajen daurin auren Mujahid da Abba Ainahin wadanda za a daurawa auren sun taere amma an kama uwar bikin mai suna Salma.

Ku shiga nan dan kallon video 

πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

#https://vm.tiktok.com/ZMFn1LDnn/

Kano - Hukumar Hisbah da ke lura tare da tabbatar da da'a tsakanin al'umma ta kama wasu matasa 19 kan halartan bikin auren jinsi daya.



 Kakakin hukumar ta Hisbah, Malam Lawan Ibrahim, ya bayyana a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, cewa matasan sun hadu ne domin shaida daurin auren wasu da ake zargin yan luwadi ne du biyu, Abba da Mujahid, jaridar Punch ta rahoto.


"Kamun ya biyo bayan wani bawan Allah ya sanar da hukumar game da auren jinsi daya da ake kokarin hadawa. "Jami'anmu da ke aiki da hedkwatar hukumar Hisbah, yankin Sharada Kano, sun isa wajen kafin a fara kulla auren.




 "Daga cikin wadanda aka kama akwai mata 15 da maza hudu. "Abba da Mujahid sun tsere jim kadan bayan jami'an Hisbah sun isa wajen daurin auren, amma wacce ta shirya bikin, Slam Usman mai shekaru 21 na a hannunmu. 



"Za a mika wadanda aka kama zuwa ga yan sanda don daukar matakin da ya kamata kasancewar yawancinsu matan sun yi ikirarin cewa an gayyace su zuwa daurin auren ne daga jihohin da ke makwabtaka. 


“Za mu tabbatar da ganin cewa an kama Abba da Mujahid.” Ibrahim ya jaddada cewar hukumar ta jajirce don kawar da duk wasu munanan dabi’u a jihar. 

0 Response to " Jami'an hukumar Hisbah sun cika hannu da wasu matasa 19 a kokarinsu na kulla auren jinsi daya"

Post a Comment