Uba ya kashe ƴarsa mai shekaru 20 sabo da ta murɗe masa mazakuta
Uba ya kashe ƴarsa mai shekaru 20 sabo da ta murɗe masa mazakuta
Rundunar ƴan sanda jihar Akwa Ibom ta kama wani mai suna Sunday Etukudo bisa zargin kashe ƴarsa mai shekaru 20, mai suna Ofonmbuk Sunday sabo da hatsaniya da ta tashi a gidan nasa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, SP Odiko Macdon, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Uyo, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa marigayiyar ta kama masa mazakuta a lokacin da aka samu saɓani, inda ya kuma yi amfani da sanda ya maka mata a kai.
Bayan aikata laifin, sai Etukudo ya binne ƴar ta sa a farfajiyar gidansa da ke kauyen Omum Unyiam a karamar hukumar Etim Ekpo a jihar domin ya rufe laifin da ya yi.
Daga baya, bayan ya shiga hannu, ƴan sandan sun tono gawar marigayiyar domin a yi bincike.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bisa ga sahihan bayanai, a ranar 9 ga Oktoba, 2022, da misalin karfe 1910, wani Ime Sunday Etukudo na kauyen Omum Unyiam a karamar hukumar Etim Ekpo, ya kashe ta ba bisa ƙa’ida ba tare da binne ƴarsa, mai suna Ofonmbuk Ime Sunday, mai shekara 20 a gidansu da ke kauyen Omum Unyiam.
“Wanda ake zargin ya yi zargin cewa an samu rashin fahimtar juna a cikin iyali, wanda ya kai ga faɗa, kuma wadda aka kashe din ta rike masa mazakuta shi kuma ya yi amfani da sanda ya buge ta a kai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta, inda kuma ya yanke shawarar binne ta a cikin kabari mara zurfi don ya rufe laifin da ya aikata,”
0 Response to "Uba ya kashe ƴarsa mai shekaru 20 sabo da ta murɗe masa mazakuta"
Post a Comment