--
Wani dan Sanda Ya bindige direban Tirela har Lahira Sakamakon Abin na goro daya hanashi a Jahar Benue.

Wani dan Sanda Ya bindige direban Tirela har Lahira Sakamakon Abin na goro daya hanashi a Jahar Benue.

 



Aminiya Hausa ta ruwaito labarin yadda wani Jami’in dan sandan Nigeria ya bindige wani direban tirela har lahira Sakamakon Abin na goro daya hanashi. Direban mai suna Aondohumba Terkula ya mutu ne sakamakon harbin da dan sandan yayi mashi akan titin Anyin dake Karamar Hukumar Logon ta Jihar Binue.




Wani ganau ya bayyana cewa abun ya faru ne a daidai shingen bincike na yan sanda wanda dan sandan me suna James Aondona ya tare direban wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Katsina ala.

Dan sandan ya nemi direban daya bashi cin hancin kudi na kimanin naira dubu uku N3,000 a yayinda shi kuma direban yace naira dubu daya da dari biyar kawai zai iya bashi N1,500 kasancewar ba cikakken lodi ya dauko ba, abin daya kawo cece kuce a tsakaninsu kenan har takaiga ya harbeshi.


Wannan abu dai ya matukar tadawa mutane hanakali kasancewar abun ya faru ne sakamakon cin hanci da rashawa da wani Jami’in dan sanda ya

0 Response to "Wani dan Sanda Ya bindige direban Tirela har Lahira Sakamakon Abin na goro daya hanashi a Jahar Benue."

Post a Comment