Falaki:Turanci Universe cike yake da ababan al'ajabi kama daga yawan duniyoyi planets da suke a warwatse ɓangorai
Falaki (Turanci: Universe) cike yake da ababan al'ajabi, kama daga yawan duniyoyi (planets) da suke a warwatse, ɓangorai (asteroid ko comets), ɗamaru (Asteroid, Kuiper da Heliosphere), watanni na duniyoyi da kuma tarin taurari.
Wannan Falakin namu kuma ɗayane daga cikin biliyoyin Falakan da suke waje. Idan ban manta ba na taɓa faɗa mana sunan namu Falakin, wato "Milky Way" a Turance. Wannan Falaki namu ya tara duniyoyi guda takwas, tareda sauran ƙananun duniyoyi da akewa laƙabi da "Dwarf Planets"; irinsu Pluto da makamantansu.
To amma meye yake faruwa a kowacce daƙiƙa a cikin wannan Falaki?
Masana kimiyyar ilmin falaki wato "Cosmologists" sunyi ittifaƙin cewa a kowacce daƙiƙa guda waɗansu abubuwa masu tarin al'ajabi suna faruwa a cikinsa,
1. Ana haihuwar taurari kimanin 3,180 a kowace daƙiƙa.
2. Daga cikin taurarin da suke wanzuwa tsawon biliyoyin shekaru, guda 900 suna fashewa yayinda makamashinsu ya ƙare.
3. Daga cikin taurarin da suka fashe ɗin ana samun 30 waɗanda suke zamowa baƙaƙen ramuka (black holes). Waɗannan baƙaƙen ramuka sunada ƙarfin majanya (gravitational force) wacce takan iya janye haske cikinsa.
4. A cikin wannan daƙiƙa guda kuma ana haihuwar duniyoyi aƙalla 150,000 a sassa mabambanta na falakin.
5. Wani abun al'ajabi kuma shine yanda wannan duniyar tamu take tafiyar nisan zango 220 (220 kilometres) a cikin falakin Milky Way a kowacce daƙiƙa guda.
6. Haske yakanyi tafiyar taki miliyan ɗari biyu da casa'in da tara (299 million metres) cikin kowacce daƙiƙa. A baya na taɓayin bayanin yanda haske yake iya tafiyar nisan zango dubu ɗari uku da ɗoriya a kowacce daƙiƙa guda.
7. Sannan rana (Sun) tana ƙona makamashin ma'adanin iska na helium kimanin ton miliyan ɗari shida (600 million tons) a kowacce daƙiƙa guda.
Dukkan waɗannan abubuwan da suke faruwa suna kasancewa ne cikin daƙiƙa guda. Wannan yasa ilmin falaki yake da faɗi sosai, ta yanda bincike akan kowanne tauraro yakan iya ɗaukar shekaru.
Daga mai Zahra katsina
0 Response to "Falaki:Turanci Universe cike yake da ababan al'ajabi kama daga yawan duniyoyi planets da suke a warwatse ɓangorai"
Post a Comment