--
Labaran Safiyar Alhamis 15/06/2023CE - 26/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Labaran Safiyar Alhamis 15/06/2023CE - 26/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Labaran Safiyar Alhamis 15/06/2023CE - 26/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.





https://hausa.bzglobalservice.com.ng/2023/06/labaran-safiyar-alhamis-15062023ce.html

Shugaba Tinubu ya dakatar Shugaban EFCC Bawa kuma an unarce shi da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka na hukumar, Mohd Umar Abba, wanda zai jagoranci harkokin ofishin shugaban hukumar ta EFCC. 


DSS ta gayyaci dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hancin da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.


Najeriya ta sake komawa ta ɗaya wajen fitar da ɗanyen mai a Afirka.


Tsohon Gwamnan Kano Ganduje na son kotu ta hana EFCC bincikensa kan bidiyon Dala.


Dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji a Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sun ceto wasu manoma 10 da aka yi garkuwa da su a jihar.


Wasu daga cikin ƴan majalisar dattawa, sunce matukar ana son magance matsalolin ƴan bindiga da sauran kalubalen tsaro sai an samu hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro.


An cafke mai sojan gona a matsayin jami’in EFCC da Sojoji.


Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Imo Douglas Acholonu ya mutu.


Ƴan bindiga sunyi garkuwa da ɗaliban jami’ar Jos (UNIJOS) su 7, a safiyar ranar Laraba.


Rudunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta damke wasu bakin haure 12 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi zamba.


Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bada umarnin karbe wasu kadarori da dukiyoyin da tsohon Gwamnan jihar Sani Bello ya sayar.


Hukumar Hajji ta Kasa tace mahajjata 75 ƴan Najeriya na ɗauke da ciki, kuma an kwantar da su a asibitoci a Makkah da Madina.


Matar da ta kashe mahaifiyarta ta India ta miƙa kanta ga ƴan sanda.


Likitoci sun kaɗu da yawaitar fyaɗe a Khartoum.


Mutane 59 sun mutu sakamakon nitsewar jirgin ruwa ɗauke da ƴan gudun Hijira kusa da Girka.


An yanke wa ata mata daurin shekaru 2 saboda zubar da tsohon ciki a Ingila.


Manchester United ta kawo karshen zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane.


Mai tsaron ragar Sifaniya David Raya mai shekara 27, ya amince ya koma Tottenham.


Wani wasan kwallon kafa na sada zumunci a garin Madalla na Jihar Neja ya rikide ya koma jimami bayan tsawa ta fado wa alkalin wasa ana tsaka da fafata wasan.

0 Response to "Labaran Safiyar Alhamis 15/06/2023CE - 26/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar."

Post a Comment