--
Labaran Yau asabar  10/06/2023CE - 21/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Labaran Yau asabar 10/06/2023CE - 21/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

Labaran Yau asabar  10/06/2023CE - 21/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.





https://hausa.bzglobalservice.com.ng/2023/06/labaran-yau-asabar-10062023ce.html

Shugaba Tinubu ya yi ganawarsa ta farko da sarakunan gargajiya daga sassan kasar nan a dakin taro na Council Chambers da ke Fadar Shugaban Kasa a Abuja.


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sake kama wasu da ake zargi da satar kayan mutane yayin rushe shaguna da ake yi a Kano.


Mataimakin gwamnan Kano ya soki wasu malaman addini da suka ga laifin gwamnatin jihar kan matakin da ta dauka na rushe wasu gine-gine.


An tsinci gawar ɗan sandan da ke kula da tsohon shugaaban majalisar Dokokin jihar Imo Wanda akayi garkuwa dashi kawanan baya.


Ƴan sanda sun kai samame gidan tsohon gwamnan Zamfara, Matawalle inda suka kwace motocin alfamar da ake zargin tsohon gwamnan ya yi awon gaba da su.


Jami’ar Azman mai zaman kanta da aka kafa a Jihar Kano da wasu sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya sun karɓi lasisinsu na fara aiki.


Wata ƙungiyar 'yan Arewa CNF, ta yi kira da a kama tsohon ministan sufurin jiragen sama a lokacin Buhari, Hadi Sirika tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya bisa zarginsa da zamba.


Rundunar 'yan sanda ta kama wani kasurgumin barawon shanu a jihar Gombe.


Ɗaya daga cikin Ciyamomi 17 da gwamnan Filato ya dakatar ya yi bore, ya koma Ofis ranar Jumu'a 9 ga watan Yuni.


Hukumar kwastam ta ƙasa, ta bayyana aniyarta ta hana shigowa da kayayyakin sawa na hannu, wadanda aka fi sani da kayan gwanjo.


Ɗanyen man Najeriya ya fara kwantai a duniya, bayan Chana, Turai da Indiya sun koma sayen na Rasha.


Darajar Naira ta sake faduwa a kasuwannin musayar kudaden ketare.


Gwamnatin Senegal ta hana 'yan adawa yin zanga-zanga.


Wani kifi ya kashe wani ɗan Rasha a kusa da wurin shaƙatawa a Masar.


Shugaban Angola ya kori ministan kula da tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke bayan gwamnati na cire tallafin man fetur.


Sojojin Tunisiya 4 sun mutu bayan jirginsu na helikwafta ya afka cikin ruwa a ƙasar.


Ana fargabar ɓarkewar kwalara a Ukraine saboda ambaliyar ruwa.


Ƴan adawar Guinea Bissau sun samu rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar.

0 Response to "Labaran Yau asabar 10/06/2023CE - 21/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar."

Post a Comment