--
Babbar magana: Yan' Shi'a Sun magantu game da ibadar Layya ta babbar Sallah......

Babbar magana: Yan' Shi'a Sun magantu game da ibadar Layya ta babbar Sallah......

Shaikh Ibrahim Zakzaky (H)


Babbar magana: Yan' Shi'a Sun magantu game da ibadar Layya ta babbar Sallah......

"...Layya mu a wurinmu wajibi ne, wajibi ne daga cikin wajibobi, matukar kana da hali dole kayi layya ba sai kaga dama ba, in kana da Rago ko kuɗin sayan Rago to layya ya zama wajibi gareka. to kuma kar kace min baka da kuɗin rago, in kana da abin da zai saya rago kamar kana da "Salula Phone" wanda yake in an sashi a kasuwa yakai dubu talatin Alhali kuma na dubu goma ma ya isa buga waya, to kana da Rago. 

Ko kana da waƴansu agogonai da ba a sawa, ko waƴansu tafka tafkan riguna da ba zaka cutu ba in ka barsu ko wasu tarkacen da yake ba za ka cutu ba in ka rabu dasu, to kana da hali kenan ba wai sai kana da tsabar kuɗi ba, kana da abun kuɗi. Saboda haka in dai layya kana da hali ya zama wajibi gareka. 

Har walayau mustahabbi ne ga wanda zai yi layya in watan ya shiga kada ya yi aski ko ya yanke farce har sai ya yi layya ɗin, Amma waɗannan ne kawai ba a ce kada ya bulbula turare ba, ko kuma ace ya yafa tufan hirami ba, illa iyaka dai abun da aka ce kenan, kada ya yi aski ko ya yanke farce har sai wannan lokacin sai ya yi kayya ɗin.

_Shaikh Zakzaky (H) Cikin Jawabinsa dangane da watan Zulhijja. a shekarun baya.

0 Response to "Babbar magana: Yan' Shi'a Sun magantu game da ibadar Layya ta babbar Sallah......"

Post a Comment