--
Dakarun kungiyar Wagner sun janye jiki daga sansanin hedkwatarta dake kudancin kasar Rasha

Dakarun kungiyar Wagner sun janye jiki daga sansanin hedkwatarta dake kudancin kasar Rasha

A daren jiya Asabar ne shugaban kungiyar sojoji mai zaman kanta ta Wagner dake kasar Rasha Yevgeny Prigozhin, ya karbi shawarar da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko ya gabatar masa, game da dakatar da matakan soja da kungiyar ta fara aiwatarwa a kasar Rasha, tare da kuma ci gaba da sassauta yanayin tashin hankali a kasar. A sa’i daya kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi alkawarin cewa, Prigozhin zai iya tafiya kasar Belarus lami lafiya, zai kuma soke karar da ya shigar game da mista Prigozhin.
Rahotanni na cewa, dakarun kungiyar Wanger sun riga sun janye jiki daga sansanin hedkwatarta dake kudancin kasar Rasha, tare da dukkanin manyan na’urorin aikin soja a daren jiya Asabar.

0 Response to "Dakarun kungiyar Wagner sun janye jiki daga sansanin hedkwatarta dake kudancin kasar Rasha"

Post a Comment