--
Sheik Yasir Ad Dawsary ne zai zai jagoranci gabatar da Sallar idin babbar  ta bana, a Masallacin Haramin Makkah, Ranar 10 ga Watan Dhul Hijjah, Shekara ta 1444, Dai-dai da 28 ga Watan Yunin shekarar 2023.

Sheik Yasir Ad Dawsary ne zai zai jagoranci gabatar da Sallar idin babbar ta bana, a Masallacin Haramin Makkah, Ranar 10 ga Watan Dhul Hijjah, Shekara ta 1444, Dai-dai da 28 ga Watan Yunin shekarar 2023.


Tarihin Sheikh Yasser Al Dosari .

Shahararren Qari ne (Mai Karatun Alkur'ani), malamin addinin Musulunci kuma limamin Masallacin Harami na Makkah . Farkon Rayuwa da Ilimi. An haifi Sheikh Yasir Al-Dosary a lardin Al-Kharj na kasar Saudiyya a shekara ta 1980 kuma yana da 'ya'ya mata biyu da maza biyu.

Farkon Rayuwa da Ilimi

An haifi Sheikh Yasir Al-Dosary a lardin Al-Kharj na Birnin Riyadh A kasar Saudiyya a shekara ta 1980 Yanzu Yana Da Shekaru 42 A Duniya kuma yana da 'ya'ya mata biyu da maza biyu.

Ya kammala haddar Al-Qur'ani yana dan shekara 15. a karkashin fitattun Shaihunai irinsu Sheikh Bakri Tarabishi, da Sheikh Ibrahim Al-Akhdar.

Yasser Al-Dosari ya sami digiri na farko a fannin Sharia a Jami'ar Imam Mohammad Ibn Saud Islamic University (IMSIU) sannan ya samu digiri na biyu a fannin Shari'a a wannan jami'a. Sannan ya sami digirin digirgir a sashen Comparative Fiqh daga cibiyar shari'a.

Sheikh al-Dossari ya samu sa'ar samun tallafi da taimako daga Shaihunan Sheikh Dr. Abdullah bin Jibreen, Shaykh Abdul Aziz bin Abdullah Al-Sheikh (Mufti a Saudi Arabia), Sheikh Dr. Saleh bin Humaid (Shugaban hukumar CSM kasar), da Sheikh Saad bin Nasser Al Shateri (wani memba na manyan masu wa'azi).

Sana'a

Sheikh Yasir Al-Dosary ya yi aiki a matsayin Babban Sakatare na kungiyar Yariman Sultan na haddar Al-Qur'ani. Ya Sami matsayin limami a masallatai daban-daban, kamar masallacin Dakhli da ke Riyadh. Shi mamba ne a Jami'ar Sarki Saud, A taron Global Europe Symposium of Muslim Youth, kuma shi ne babban sakataren jami'ar Yarima Sultan na koyar da kur'ani ga sojojin tsaron Saudiyya.

Daga: Saliadeen Sicky

0 Response to "Sheik Yasir Ad Dawsary ne zai zai jagoranci gabatar da Sallar idin babbar ta bana, a Masallacin Haramin Makkah, Ranar 10 ga Watan Dhul Hijjah, Shekara ta 1444, Dai-dai da 28 ga Watan Yunin shekarar 2023."

Post a Comment