--
kasar Sweden ta bayar da izinin yin gangamin ƙona littafin Injila da Attaura

kasar Sweden ta bayar da izinin yin gangamin ƙona littafin Injila da Attaura‘Yan sandan Sweden sun bayar da izinin gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Stockholm a ranar Asabar, inda mai shirya taron ya ce za su kona kwafin Attaura da Injila.

Wata mai magana da yawun 'yan sandan ta jaddada wa BBC cewa izinin na gudanar da gangami ne kawai, ba domin a yi wani abu na daban ba.

Hakan ya biyo bayan wani gangami da aka yi, inda aka kona Al-kur'ani a wajen wani masallaci a birnin na Stockholm, a watan jiya.

Sweden tana da dokar bayar da ƴancin faɗin albarkacin baki da gudanar da gangami.

Shugaban Isra'ila ya yi Allah wadai da izinin.

Isaac Herzog ya ce ya soki ƙona Alkur'anin da aka yi, kuma a yanzu yana jin takaicin hakan zai iya kasancewa a kan littafi mai tsarki na Attaura.

Credit:Bbchausa

0 Response to "kasar Sweden ta bayar da izinin yin gangamin ƙona littafin Injila da Attaura"

Post a Comment