--
Da Dumi Duminsa Kasashen Mali, Burkina da Guinea sun lashi takobin shigarwa Nijar fada da Ecowas

Da Dumi Duminsa Kasashen Mali, Burkina da Guinea sun lashi takobin shigarwa Nijar fada da Ecowas



Kasashen Burkina Faso da Mali, da Guinea, sun bayyana duk wani yunkuri na amfani da karfin soji wajen dawo da zababben shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum a matsayin kaddamar da yaki a kansu.

Hakan ya biyo bayan barazanar da shugabannin kasashen yankin yammacin Afirka ECOWAS suka yi ta yin amfani da karfi wajen maido da tsarin dimukradiyya kasar idan har jami'an soji a Yamai suka ki mayar da hambararren shugaban kasar.

Dukkan kasashen uku that ke karkashin mulkin soja a halin yanzu, makwabta ne da Nijar, suna fama da matsala iri daya, wato matsalar tsaro

A yanzu, an iya cewa yanayin, kuma wannan mataki na kasashen uku na iya sake dagula al’amura matuka gaya, ake ciki na kara zafafa


shugabannin soji na Mali da Burkina Faso, sun yi barazanar cewa, idan kungiyar ECOWAS ta shiga tsakani ta hanyar soji a Nijar, to za su kawar da kungiyar daga yankin dungurungum.

Sun ce tura soja, zai zama bala'i da haifar da rashin zaman lafiya.

Kasashen biyu dai sun yanke hulda da kasashen ECOWAS tare da rungumar sabon kawance da Rasha.

Faransa ce ta yi musu mulkin mallaka, sai dai a yanzu sun sanya zare da ita, musamman ta fuskar yaki da matsalar masu ikirarin jihadi, kuma kamar Nijar.


Daga BBC Hausa


0 Response to "Da Dumi Duminsa Kasashen Mali, Burkina da Guinea sun lashi takobin shigarwa Nijar fada da Ecowas"

Post a Comment