--
Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da kashe fiye da mutum 16 da ceto mutane da dama a jihar Katsina

Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da kashe fiye da mutum 16 da ceto mutane da dama a jihar Katsina


Rundunar sojin sama ta “Operation Hadarin Daji” sun yi luguden wuta a sama a sansanonin kasurguman ‘yan bindiga Ado Aliero da Dankarami a jihohin Katsina da Zamfara, inda suka samu nasarar kashe ‘yan bindiga sama da 16 a lokacin da suka kai hare haren.

“A rahoton da Katsina Reporters ta samu na cewa sojojin sun yi luguden wutar ne a tsakanin ranar 28 da ranar 29 ga watan Yulin 2023, a sansanonin ƴan bindigar daban-daban a ƙananan hukumomin Faskari da Jibia a jihar Katsina da kuma garuruwan Zurmi, Tsafe na jihar Zamfara. 

Sojojin sun yi luguden wutar ne, bayan samun bayanan sirri cewa, Ado da yaransa sune a ƙwanan baya suka sace mutane da wasu Shanu a Tsafe da Faskari da garin Jibia na jihar Katsina. 

Haka zalika, sojojin sun kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan mai suna Danƙarami da yaransa tare da lalata sansanin.

A cikin jawabin Kakakin rundunar ta sojin sama “Komodo Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai harin a sansanan na ‘yan bindigar biyu.

0 Response to "Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da kashe fiye da mutum 16 da ceto mutane da dama a jihar Katsina"

Post a Comment