Yau ne kungiyar ƙwadago a fadin Najeriya ke fara zanga-zanga ta ƙasa baki daya don nuna rashin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnati tayi
zanga-zanga ta ƙasa baki daya don nuna rashin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnatin nageria tayi.
Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa `yan kasar dangane da halin matsi da matakin ya jefa su ciki, amma ya ce babu wani zabin da ya fi janye tallafin, kana ya sanar da wadansu matakai da gwamnati ta dauka don rage radadin janye tallafin.
Sai dai kungiyar kwadagon ta ce babu wani tasiri da za su yi wajen rage wa al`umma ukuba.
Jiya Talata shugabannin ƴan kwadagon sun yi zama da wakilan gwamnati a fadar shugaban kasa, sai dai ba a cimma komi ba.
Comrade Nasir Kabir, shi ne jami`an tsare-tsare na kungiyar kwadago ta kasa a Najeryar, ya kuma shaida wa BBC Hausa cewa har yanzu basu gamsu da abun da gwamnati ke cewa ba, don haka yau din nan mambobinsu na jihohi 36 za su fara wannan zanga-zanga.
Ya ce ''Duk duniya babu inda gwamnati ba ta bayar da tallafi, amma sia nan Najeriya ne lokaci daya zai kai dari shida da wani abu, muna cikin tattaunawa aka aka je aka sake daga farashin man, mu muna ganin gwamnati wasan kwaikwayo take yi, ta fito ta fadi sunan wadanda ake cewa sune suke morar kudin tallafin man nan''
Ya ci gaba da cewa sun y alkawari da gwamnati kan inganta matatun mai da ake da su da kuma samar da wutar lantarki, amma ko daya babu wanda aka cika har yanzu.
A cewarsa ''Yaudara ce wannan, idan ma akwai wani tallafi da ake biya me yasa ba janye ba tuntuni?''
Ya ce sun sanar da dukkan hukumomin tsaro game da zanga-zangar ta yau, don haka suna fatan jami'an za su ba su cikakkiyar kariyar da doka ta ba su''.
Bukatun da NLC ke son a biya mata
Kimanin bukatu guda shida ne kungiyar yan kwadagon ta bukaci mahukuntan Najeriya su biya mata, ga wasu daga cikinsu.
1- Aiwatar da yarjejeniyar da aka amince da ita tsakanin gwamnati da ƴan kwadago da majalisa da kuma TUC
2- Janye dokoki masu tsauri da aka sanya, ciki har da na janye tallafin mai da kara farashinsa
3- Gyara matatun man fetur na Warri da Kaduna da kuma Fatakwal.
4- Biyan albashin watanni takwas na malamai da ma'aikatan jamio'i
0 Response to " Yau ne kungiyar ƙwadago a fadin Najeriya ke fara zanga-zanga ta ƙasa baki daya don nuna rashin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnati tayi"
Post a Comment