--
Kotun Sauraron Karar Zaben Gwamnan Jahar Kano ta Soke Nasarar Abba Kabir Yusuf Ta Ayya Nasiru Yusuf Gawuna a Matsayin Gwamnan Jahar

Kotun Sauraron Karar Zaben Gwamnan Jahar Kano ta Soke Nasarar Abba Kabir Yusuf Ta Ayya Nasiru Yusuf Gawuna a Matsayin Gwamnan Jahar



Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.

Jam'iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir, bayan hukumar zaɓe ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen 18 ga watan Maris na 2023.

Kotun ta bayyana wannan hukunci ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro.

Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay, shugabar kotun mai alƙalai guda uku.

0 Response to "Kotun Sauraron Karar Zaben Gwamnan Jahar Kano ta Soke Nasarar Abba Kabir Yusuf Ta Ayya Nasiru Yusuf Gawuna a Matsayin Gwamnan Jahar"

Post a Comment