--
Kotun zabe ta tabbatar da Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Bauchi

Kotun zabe ta tabbatar da Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Bauchi


Kotun sauraron ƙorafin zaben gwamna a jihar Bauchi ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A game da haka, kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna, tsohon babban hafsan sojin sama, Sadique Abubakar suka shigar.

Ta ce babu wani kwaƙƙwaran dalili na soke zaɓen saboda an gudanar da shi ne bisa ƙa'ida.

A watan Maris ne INEC ta bayyana cewa Bala Mohammed ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Sadique Abubakar.

0 Response to "Kotun zabe ta tabbatar da Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Bauchi"

Post a Comment