A wani yunƙuri na neman matsaya Kan Rikicin Hamas da Isra’ila Saudi Arabiya ta kira taron gaggawa na Ƙasashen Ƙungiyar OIC su 57
Ministan Harkokin Wajen kasar Iran Hossein Amirabdollahian ya sake jaddada cikakken goyon bayan ƙasar ga ƙungiyoyin Hamas , yayin da ya yi kira a magance ɓarkewar mummunan yaƙi a yankin baki ɗaya.
“Tirjiya ga rashin adalci da ƙuntatawa abu ne da za a iya ci gaba da shi kuma za a iya ɗaukar kowane irin mataki.” Inji shi.
Haka ya shaida wa manema labarai a Beirut, babban birnin kasar Lebanon.
Ya ce ya gana da Shugaban Ƙungiyar Hamas da na sauran ƙungiyoyin sa-kai daban-daban.
“Mun tattauna duk abin da zai iya yiwuwa, kuma kowane hannun sa a kan kunamar bindiga ya ke, ƙyas kawai ya ke jira.”
Amirabdollahian ya sake yin gargaɗi ga Isra’ila cewa ta daina jefa bamabamai kan yankin Gaza, ko kuma a yi ta ta ƙare, a ilahirin yankin baki ɗaya.
Sai dai kuma duk da haka ya ce Iran ta yarda a sasanta ta hanyar diflomasiyya, ko kuma a yamutse.
“Har yanzu ƙofar sasantawa a buɗe ta ke, amma idan lamarin fa ya ƙara ɗaukar lokaci Isra’ila ta ci gaba da kai wa Gaza hari, to an yi latti fa.”
Ba a ga-maciji tsakanin Iran da Isra’ila tun cikin 1997 shekarar da Iran ta yi Juyin Turun Musulunci.
A ranar Asabar Amirabdollahian ya gana da Shugaban Hamas, Isma’il Haniyeh, a Doha, babban birnin Qatar.
Shekaru 15 kenan Qatar na goyon bayan Falasɗinu, kuma yanzu haka ta na bada tallafi ga al’ummar Falasɗinu kuma ita za ta sake gina wa Falasɗinu wuraren da Isra’ila ta ragargaza mata.
Shi kan sa Shugaban Hamas Ismail Haniyah a ƙasar a Qatar ya ke ciki.
Saudiyya Ta Kira Taron Gaggawan Ƙasashen Musulmi 57:
A wani yunƙuri na neman matsaya ɗaya, Saudi Arabiya ta kira taron gaggawa na Ƙasashen Ƙungiyar OIC su 57.
Za a yi taron a Riyadh, babban birnin Saudiyya a ranar 18 da 19 ga Oktoba. Ƙasashe 57 ne a ƙungiyar OIC.
0 Response to "A wani yunƙuri na neman matsaya Kan Rikicin Hamas da Isra’ila Saudi Arabiya ta kira taron gaggawa na Ƙasashen Ƙungiyar OIC su 57"
Post a Comment