--
DALILIN DAYA SA AKA DAKATAR DA SHIRIN N-POWER NA WUCIN GADI

DALILIN DAYA SA AKA DAKATAR DA SHIRIN N-POWER NA WUCIN GADI

Minista ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa wasu masu kula da shirin na riƙe da kuɗaɗen matasan da ke amfani da shirin, kuma kwantiraginsu ta ƙare a watan Maris na 2023 ba tare da sabunta komai ba. 

Ministar ta kuma bayyana cewa wasu da suka ci gajiyar tallafin suna yin wasu ayyuka amma har yanzu suna cin gajiyar shirin, yayin da wadanda suka yi aiki da gaske ba a biya su ba.

Ta kuma ce an dakatar da shirin ne saboda akwai bukatar a tantance adadin mutanen da ke cikin shirin, da waɗanda suka fice daga shirin, da wadanda suke bin basussuka, ko sun je wuraren aiki ko ba su je ba, da kuma yadda aka yi amfani da kudade a kan shirin.

Ministan ta kuma ce za a faɗaɗa shirin domin ɗaukar ƴan Najeriya miliyan biyar nan da shekaru biyar masu zuwa. Baya ga haka, ta kuma ce za a sake duba ɓangaren ƙayyade shekarun masu cin gajiyar shirin zuwa shekaru 18-40 saɓanin yadda tsarin yake a baya na 18-35. 

Ahmed Rufai Idris 
National Chairman NIGERIAN YOUTH OPPORTUNITIES

0 Response to "DALILIN DAYA SA AKA DAKATAR DA SHIRIN N-POWER NA WUCIN GADI"

Post a Comment