--
INEC:Bamu janye ɗaukaka ƙara akan shari'ar zaɓen gwamnan Kano ba

INEC:Bamu janye ɗaukaka ƙara akan shari'ar zaɓen gwamnan Kano ba

 

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta musanta cewa ta janye ɗaukaka ƙarar da tayi akan shari'ar zaɓen gwamna ta jihar Kano, inda tace takardar da ake yaɗawa mai dauke da sa hannun wani jami'in shari'a na reshen hukumar dake Kano, ba takarda ce wacce ta fito a hukumance ba.

INEC ta bayyana haka ne cikin wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, mai dauke da sa hannun babban kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan al'umma akan zaɓe, Sam Olumekun, inda ta bukataci al'umma da suyi watsi da waccan jita-jita da ake yaɗawa. 

Sanarwar ta ƙara da cewa, tuni hukumar ta bawa lauyoyin ta dama akan suyi dukkan abinda ya dace, wanda bai ci karo da tsare-tsaren ta ba. 

Credit NasaraRadio

0 Response to "INEC:Bamu janye ɗaukaka ƙara akan shari'ar zaɓen gwamnan Kano ba "

Post a Comment