--
Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta cafke wasu Littattafai masu kalamai na batsa

Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta cafke wasu Littattafai masu kalamai na batsa


Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano, karkashin jagorancin Abba Al-Mustapha, ta dakatar da sayar da Littafin Queen Primer tare da kira ga Malaman Makarantu da su guji amfani dashi.

Hakan ya biyo bayan bincike da hukumar tayi bisa korafe-korafe da aka kawo kan yadda ake zargin Littafin da wasu kalamai na batsa, waɗanda bai kamata ba ga al'umma da kuma rayuwar yara.

Daga karshe hukumar tayi kira ga malamai da kuma shugabannin Makarantu da su guji amfani da wannan Littafi  ko doka tayi aiki akan su.

Credit: Rahamatv

0 Response to "Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta cafke wasu Littattafai masu kalamai na batsa"

Post a Comment