Shin Katafa Samun Matsala da wani banki ya cutar da kai ga yadda zaka tuntubi CBN domin samun mafita
Kwanaki biyu da suka gabata wani dan uwa yayi bayanin yadda ya kai karar wani banki a CBN kuma an dauki mataki an mayar masa da kudin sa.
Naga dayawa sunyi tambayar yadda zasuyi irin wannan korafin.
Toh CBN dai sunyi bayani dalla-dalla.
1. Idan kanada wani korafi, toh dole bankin ka zaka fara yima korafi. Zaka ba bankin naka har sati biyu domin warware matsalar.
2. Idan akayi sati biyu bankin naka basuyi komai ba, toh zaka iya sanarda sashen kare hakkin kwastomomi na CBN, wato Customer Protection Department.
3. Haka zalika, idan banki naka su ka kasa kula sakon ka har kwanaki 3, ko suka kasa baka lambar shedar karbar koken ka (wato reference number) toh nan take zaka iya yada korafin ka zuwa shashen kula da hakkin kwastomoni na CBN, wato ta hannun Darakta na shashen.
4. Zaka sanar da CBN ne kawai idan bankin naka ya kasa yin abinda ya dace kamar yadda akayi bayani a baya (1 & 2)
5. Idan bukatar korafi ta kama, zaa rubuta wasika zuwa ga wannan adireshi
The Director, Consumer Protection Department, Central Bank of Nigeria, Central Business District, Garki, Abuja.
Dole ne wasikar taka ta kasance zuwa ga Darakta, Shashen kare hakkin kwastoma, wato Director Consumer Protection Department
➡️ Zaka kai wasikar taka a offishin CBN mafi kusa gareka.
Zama ka iya tura sakon email ➡️Email: cpd@cbn.gov.ng
Idan ka amfana, kayi sharing domin wasu su amfana
Ga bayanin a cikin turanci kamar yadda CBN din ta wallafa
0 Response to "Shin Katafa Samun Matsala da wani banki ya cutar da kai ga yadda zaka tuntubi CBN domin samun mafita "
Post a Comment