--
Kisan Masu Maulud a jahar kaduna:Mun tabbata Sojoji suna ƙoƙari wajen kare rayukan mutanen ƙasa

Kisan Masu Maulud a jahar kaduna:Mun tabbata Sojoji suna ƙoƙari wajen kare rayukan mutanen ƙasa

Suna kutsawa haɗari, suna rasa rayukansu domin neman kiyaye rayukan talakawa.

Sai dai akwai matuƙar sakaci wajen samar masu da dukkan abubuwan da suke buƙata domin gujewa tafka kurakurai cikin hareharensu ga ɓarayin jeji da sauran miyagu.

Babu shakka an yi ƙazamar aika-aika a Kaduna a kan masu Maulidi da basu yi kama da ƴan ta'adda ba ta kowace fuska, kuma za a iya kaucewa faruwar irin wannan aika-aika idan an bi matakan da suka dace.

Ya wajaba hukuma ta ɗauki alhakin biyan diyyar waɗanda suka rasa rayukansu da maganin waɗanda suka jikkata.

Muna fata wannan kuskure ba zai sanyaya gwiwar sojojinmu ba wajen ganin sun tsaftace dazukanmu daga ɓarayin jeji da sauran ƴan ta'adda. 

Kamar yadda muke fata, hukuma zata miƙe tsaye wajen tabbatar da ƙananan sojoji suna samun duk irin horo da makamai da suke buƙata domin taƙaita kurakurai wajen aiwatar da aikinsu.

Kamar yadda Prof. Ibrahim maqari ya bayyana a shafinsa na Facebook. 

0 Response to "Kisan Masu Maulud a jahar kaduna:Mun tabbata Sojoji suna ƙoƙari wajen kare rayukan mutanen ƙasa"

Post a Comment