--
Shawara ta Ga yan uwana Matasa

Shawara ta Ga yan uwana Matasa

 


Shawara ga yan uwa na Matasa

Assalamu alaikum, wannan shawara ce ga yan uwana matasa musamman masu yawan amfani da social media,

Mutane da dama suna ganin cewa a yanzu duk wani abu da zaa ce an bude ana cikewa al-ummar mu musamman Yan arewa sai ka ga sun kau dakai  bazasu cike ba, sai kuma abun yazo yatabbata sai kaji mutum yanacewa  ina ganin  abun naki cikewa.

Haryanzu akwai damarmaki a kasar nan da wajan kasar nan kamar irin abunda ya shafi


  •  Full Scholarship
  • Jobs +NGO
  • Grants/loan.
  • Free courses da sauran su

Zan bada misali akaran kaina

Zan dauki daya scholarship ina kokarin cike abunda yashafi sha’anin scholarship  duk wanda naga inada requirements din cikewa, kuma Alhamdulillah, akan wannan tsarin kwanakin baya na sami full scholarship a akasar Algeria wani abu yasa ban sami damar tafiya, haka kuma nakara samun admission a saint louis university  akasar Spain shima dai bansamu naje ba, haka akasar India, but wanda a yanzu haka ina karatun Master of Computer Application a kasar india a makaranta Indira Gandhi national open university india wanda shima full scholarship ne, abunda nake so yan uwana su gane cewa irin wannan damar makin basai ka san wani ba  MAI NEMA YANA TARE DA SAMU kar mu gajiya.

Haka akan abunda yashafi ayyuka, nasami invitation da dama a akan abunda yashafi NGO wasu naje wasu kuma uziri ya hanani zuwa, kuma batare dana san wani ba, recently wanda nasamu a kampanin AA rano naga email a na turawa na tura kuma cikion ikon Allah batare da nasan wani ba aka kirani interview kuma ake gaya min cewa a duk local government mutum biyar aka kira, tambayar da aka fara min sai cewa akai waya turo ka nace babu kowa

Duk da nasan kasar tamu, wani lokacin in baka san wani ba aiki yana wahalar samuwa, amma kuma wannan bashi zai hana ka kace kadaina cikewa ba, wanda alhamdulilah nasan mutane da dama wanda suka sami aiki musamman aikin force cikewa kawai sukai kuma suka samu, haka tsarin N-power  haka grant da irin su nirsal da sauran su

Haka kuma abunda yashafi free courses /professional certificate kada mu raina duk wani course daka ji za ai kuma zaa bada certificate yikokari kayi zasu taimakawa CV dinka wajan neman aiki ta yanda da ka tura cv dinka zaayi saurian regarding dinka fiye da wanda bashi dashi, i have more than 50 certificate, amma duk da haka muna kara cigaba da yi, 

Sai ka ga graduate amma CV din shi ko shi aka ce yabawa kan sa aiki sai yaji kunya babu working experience babu skills babu publication babu professional certificate, da sauran su

Dan haka dan uwa kada kadamu yau ka cike baka samu ba wata ran zaa dace,

Umar Mustapha Usman

CEO UMtech Computer Services0

7067129377

1 Response to "Shawara ta Ga yan uwana Matasa "

  1. Gaskiya shawararka abace mai mutuqar amfani wanda kusan ni kaina irin wadan nan shawarwarin naka na zama shaida akansu. Bana wasa wajen cike portal, kuma cikin nasara wani abun na dace wani kuma ace muni try again later.
    Jazakallah be jannatul firdaus

    ReplyDelete