Masu Kwalin OND, NCE, Diploma, HND, BSc. MSc. da Ph. D an Bude Shafin Daukar Ma'aikata a Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC)
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ita ce cibiyar kula da lafiyar jama'a ta kasa da ke da alhakin jagorantar rigakafi, ganowa da shawarta da martani ga barkewar cututtuka a Najeriya.
A wannan karon cibiyar ta fitarda sabin ayuka a bangarori daban- daban ga masu kwalin masu kwalin OND, NCE, Diploma, HND, BSc. MSc. da Ph. D.
Ayuka da aka bude
Ayukan da aka buda sun hada da:
1. Administrative Officers
2. Administrative Officers CMUL
3. C19RM Health Product Management and Logistics (HPML) Specialist
4. HAI Surveillance Consultant
5. IPC Guideline Development Consultant
6. IPC Project Manager
7. IT Assistant
8. IT Assistant CMUL
9. Monitoring and Evaluation Officers
10. Training Consultant
Ranar Rufe Cikewa
Kamar yadda hukumar ta fitar za'a rufe shafin daukar sabin a ma'aikata a bangarori da aka lissafa a sama a ranar 17th April, 2024.
Yadda Zaku Cike
Masu shawar cike gurabun da aka lissafa, ku latsa shafin yanar gizo-gizo dake a kasa
https://career.ncdc.gov.ng/jd_email.php?r=job_form
Karin Bayani Akan Yadda Zaku Cike
Bayan kun danna mahadar adireshin da ke sama, zungura ƙasa zuwa inda aka rubuta " Verification Form." Sannan shigar da sunan farko da adireshin imel, sannan ku jira kadan. Za a aika sanarwar tabbatarwa zuwa adireshin imel ɗinku kamar "To continue your registration, please click on the verify email button below. Sannan ku danna "Verify Email" don ci gaba da aikace-aikacenku. Dole ne mu tabbatar munyi submitting na CV da Cover letter.
0 Response to "Masu Kwalin OND, NCE, Diploma, HND, BSc. MSc. da Ph. D an Bude Shafin Daukar Ma'aikata a Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC)"
Post a Comment