--
Anbude shafin Rajistar Shirin TVET - Kuje ku cike yanzu

Anbude shafin Rajistar Shirin TVET - Kuje ku cike yanzu


Kira Ga Masu Sha'awar Rajistar Shirin TVET - NBTE Ta Bude Shafi Don Cikewa Hukumar Kula da llimin Fasaha da Sana'o'i (NBTE) tare da Ma'aikatar llimi ta Tarayya tana kira ga Cibiyoyin Horas da Sana'o'i (STCs), Makarantun Sana'a (VEls), da Masana Sana'a (MCPs) da su yi rajista don tantancewa. Wannan shiri na TVET zai bai wa 'yan Najeriya damar samun kwarewar sana'a mai amfani.

Abubuwan da ake Bukatu Domin yin Rajista:

1. Makarantun Sana'a (VEIs)

- Dole ne su kasance da rajistar CAC

- Su bi tsarin karatu na NSQ.

-Akalla malami guda daya ga dalibai 40.

- Su mallaki QAA da IQAM ko su dauki ma'aikata na wucin gadi.

2. Cibiyoyin Horas da Sana'a (STCs)

-Su kasance da rajistar CAC.

- Malami mai kwarewa ko wanda ke da NSQ Level 3.

- Su mallaki QAA da IQAM.

3. Masana Sana'a (MCPs)

- Su kasance da rajistar CAC ko NIN

- Su bi tsarin NSQ.

-Su mallaki malami ko masanin sana'a mai NSQ

Level 3.

-Su kasance da dakin koyarwa da bayanan horo na baya.

Ku latsa nan Yanzu domin yin Register: https://www.digitalnbte.nbte.gov.ng/TVET/TVETApplication2

0 Response to "Anbude shafin Rajistar Shirin TVET - Kuje ku cike yanzu"

Post a Comment