
Yanzu yanzu: Anga Jinjirin watan Qaramar Sallah Kai tsaye Daga Ofishin Jagoran 'Yan Shi'a Sheikh Ibraheem Zakzaky | Duba Cikakkun bayanai
Yanzu yanzu: Anga Jinjirin watan Qaramar Sallah Kai tsaye Daga Ofishin Jagoran 'Yan Shi'a Sheikh Ibraheem Zakzaky | Duba Cikakkun bayanai
Kamar yadda aka wallafa a Shafin facebook na Jagoran 'Yan Shiga a Najeriya cewa AN GA JINJIRIN WATAN SHAWWAL!
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على سيدنا محمد وآله الطيبين الطاهرين
Ya zuwa yanzu haka mun sami tabbacin ganin jinjirin watan Shawwal a Nguru, Potiskum, Damaturu, Geidam da Babban Gida duk a Jihar Yobe da Bajoga (a wani ƙauye mai suna Wawa) a Jihar Gombe. Har wa yau kuma an gani a wani gari mai suna Saran Dosa a Jihar Kebbi.
Har yanzu dai labarai na isowa garemu kuma muna ƙoƙaarin tantancewa. A duk waɗannan wurare jama'a masu yawa ne suka gani. Don haka gobe Lahadi ta zama 1 ga watan Shawwal 1446, in sha Allah.
Allah Ta'ala Ya amshi ayyukan ibadodinmu da addu'o'inmu. Ya kuma maimaita mana na shekaru masu zuwa cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki.
@Szakzakyoffice
#Eidmubarak
#PrayForPalestine
#OurMartysOurHeroes
29 Ramadan 1446
29/03/2025
0 Response to "Yanzu yanzu: Anga Jinjirin watan Qaramar Sallah Kai tsaye Daga Ofishin Jagoran 'Yan Shi'a Sheikh Ibraheem Zakzaky | Duba Cikakkun bayanai"
Post a Comment