--
Shirye-Shiryen Gwamnatin Tarayya 5 da Zasu Amfanar da Matasa Karkashin Renewed Hope Agenda – Ka Cika Naka Yanzu

Shirye-Shiryen Gwamnatin Tarayya 5 da Zasu Amfanar da Matasa Karkashin Renewed Hope Agenda – Ka Cika Naka Yanzu

Shirye-Shiryen Gwamnatin Tarayya 5 da Zasu Amfanar da Matasa Karkashin Renewed Hope Agenda – Ka Cika Naka Yanzu!



A kokarin da gwamnatin tarayya ke yi don tallafa wa matasa da masu sana’a, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da muhimman shirye-shirye guda biyar karkashin Renewed Hope Agenda. Waɗannan shirye-shiryen sun shafi sana’a, horo, aikin yi da ƙarfin kasuwanci. Ga bayani a kan kowanne:

1️⃣ TVET (Technical and Vocational Education and Training)

Manufa: 

Taimakawa matasa da ilimi da horo na sana’o’i domin dogaro da kai. Ana koyar da sana’o’in hannu, fasaha da dabaru don shiga kasuwa.

2️⃣ YEIDEP (Youth Empowerment and Innovation Development Program

Manufa:

 Horas da matasa kan kirkire-kirkire da bunkasa kasuwancin sabbin ra’ayoyi. Ana tallafa wa masu sha’awar fara kasuwanci da horo da jari.

3️⃣ LEEP (Local Empowerment and Employment Program)

Manufa: 

Samar da ayyukan yi ga matasa a matakin ƙananan hukumomi. Wannan shiri yana da nufin rage zaman banza da samar da kudin shiga ga matasa a yankunansu.

4️⃣ NATEP (National Talent Export Program)*

Manufa:

 Fitar da ƙwararrun matasa zuwa kasashen waje don aikin yi. Ana horar da su a fannoni kamar ICT, aikin lafiya, injiniya da sauransu.

5️⃣ GIGS (Government Information & General Services)

MANUFA: 

Samar da ayyukan wucin gadi ko freelance ga matasa. Masu rajista za su samu damar shiga ayyukan dijital da aiki daga gida.

Kira Ga Jama’a:

Kada ka bari a bar ka a baya! Wannan dama ce da gwamnati ta tanada domin tallafa wa rayuwar matasa da masu sana’a a fadin Najeriya. Duk shirye-shiryen kyauta ne, kuma suna da rajista ta yanar gizo wacce ke buɗe a halin yanzu.

✅ Yi amfani da wayarka ko kwamfutarka  

✅ Cika fom ɗin da ke shafin kowane shiri  

✅ Jira amsa ko kiran shiga horo ko tallafi

Ka Rarraba Wannan Bayanin Ga Abundant

0 Response to "Shirye-Shiryen Gwamnatin Tarayya 5 da Zasu Amfanar da Matasa Karkashin Renewed Hope Agenda – Ka Cika Naka Yanzu"

Post a Comment