An Haramta zancen dare ga Samari Da 'Yan Mata A jihar Kano, Duba dalili
Hoto: Bar. Bulama Bukarti Source: Aminiya Daily Trusy |
A Jihar Kano an haramta wa masoya haduwa a domin gudanar da zancen dare a karamar hukumar Rano ta jihar Kano,
Dokar da aka kafa ta samo asali ne sakamakon rahotannin da ake samu na ayyukan lalata tsakanin 'yan mata da Samari maza.
A cewar jami'in watsa labarai na karamar hukumar Rano, Habibu Faragai, shugaban majalisar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar a wani taron kwamitin tsaro da mazauna yankin da shugabannin gargajiya suka halarta.
Mista Muhammad ya ce kwamitin ya tayar da jijiyoyin wuya kan yawaitar lalata a karamar hukumar,
Ya ce an sanya dokar ne don tsaftace yankin na hana ayyukan lalata da ke faruwa yayin tattaunawar dare tsakanin Samari da 'Yan Mata A Yankin,
Shugaban majalissar ya umarci hukumar Hisbah ta jihar da ('yan sandan) da sauran jami'an tsaro a matakin karamar hukuma dasu tabbatar da anbi dokar da kama masu aikata laifuka.
0 Response to "An Haramta zancen dare ga Samari Da 'Yan Mata A jihar Kano, Duba dalili"
Post a Comment