--
Kalli Bidiyon Baturiyar da tayi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta

Kalli Bidiyon Baturiyar da tayi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta


Wata budurwa ta bar kasar ta Rasha ta dawo nan gida Najeriya saboda sha’awar wasan barkwanci na ban dariya da ake yi anan wanda tuni ya dauki hankalinta.


Juliana Belova ita ce budurwar ta ba da mamaki bisa nuna ra'ayin da ba a saba ji ba, kasancewar mutane da dama na son barin Najeriya zuwa turai, amma ita ta baro turai zuwa Najeriya mai cike da albarka. Meye dalilin da yasa ta yanke wannan shawara mai kyau? 


A wata hira da aka yi da ita a shirin TVC mai suna Wake Up Nigeria, budurwar da aka fi sani da 'Oyibo Marlian' ta bayyana cewa kawai ta fada matukar kaunar wasan barkwanci na ban dariya na Najeriya ne. 


Oyibo Marlian' ta ce yayin da take a kasar Rasha, ta yi sha'awar yadda ake sarrafa salon wasan kwaikwayo na ban dariya wanda ya sha bamban da abin da ake samu a kasar haihuwar ta; Rasha ko Amurka. 


Juliana ta ce ta kan kalli wasan barkwanci a tsawon lokaci a kan kafar sada zumunta na kawayenta 'yan Najeriya don haka ta yanke shawarar ta dawo gida Najeriya da zama. 


Da jakarta da kudi N41,000 kacal ta shigo Najeriya Juliana, a cewar rahotannin Vocal Media, ta bar Rasha daga ita sai jakar kayanta da kudi $100 (N41,000) kasancewar ta rasa aikinta a lokacin barkewar cutar Korona. 


Kudin da ta zo Najeriya da shi an ce wani dan a-mutun ta ne ya ba ta a kafar sada zumunta ta Instagram. Abin da take yi a Najeriya 


Gaskiyata kalamanta, tun zuwanta Najeriya, budurwar ta tsunduma cikin harkar wasan barkwanci, tana burge mabiyanta na kafafen sada zumunta na zamani lokaci zuwa lokaci inda take daura bidiyon rawa na wasan barkwanci. 


Oyibo Marlian', kamar yadda ake kiranra, ta iya yaren Pidgin kuma an ce tana matukar kaunar wakokin mawakiyar Najeriya Naira Marley kuma ta nuna hakan a cikin raye-rayen da take yadawa. 


Tana da mabiya sama da dubu 100 a shafinta na Instagram, Juliana ta yi wasanni tare da shahararre Don Jazzy da sauran masu wasan barkwanci na A-list ciki har da Lord Lamba. 

Kalli Bidiyon Jawabinta Datayi:

0 Response to "Kalli Bidiyon Baturiyar da tayi hijira daga turai zuwa Najeriya da N41k a hannunta "

Post a Comment