--
Rashin aikin dazanyi yasanyani ajiye digirina a gefe na  kama sana'ar siyar da abinci - Inji Kyakkyawar budurwa

Rashin aikin dazanyi yasanyani ajiye digirina a gefe na kama sana'ar siyar da abinci - Inji Kyakkyawar budurwa


Wata matashiyar budurwa ‘yar shekara 23, mai suna Chizitere Daniel Vivian, ta bayyana cewa rashin aikin yi ne ya sakata fara sana’ar toya cin-cin ta kuma dauka ta sayar akan tituna.


Dalibar wacce ta karanci fannin ilimin yanayi da tsare-tsare, a jami’ar jihar Legas, ta ba wa ‘yan Najeriya shawarar su dai na dogaro da kwalin digiri, ko kuma su tsaya jiran gwamnati ta basu aiki.


Matashiyar ta bayyana hakan ne a yayin zantawar ta da wakilin legit.ng Adeoye Adewunmi a ranar litinin 16 ga Agusta.


Ta bayyana cewa sana’ar cin-cin tana rufa mata asiri sannan tana iya siyan abubuwan da a baya bata iya saya.Matashiyar ta baiwa matasan Najeriya shawarar dogaro da kai da kuma hanyar da zasu samu na kansu ba tare da jiran gwamnati ta basu aiki ba.


Ta bayyana cewa:


“Ba zanyi karya ba cewa rashin aikin yi a kasar nan ne ya saka ni fara neman na kaina.

Na yanke shawarar fara sai da cin-cin ne saboda ina son harkar girke-girke sannan ina son yiwa mutane girki.“


Yanzu haka wannan kasuwancin na cigaba da bunkasa, kuma ina iya sayen duka abubuwan da nake so a lokacin dana ke so.


To shawara ta ga masu digiri ‘yan uwana da su san abinda suke so a rayuwa su tashi tsaye su nemi abinda ya fi musu, ba wai su tsaya suna jira gwamnati ta basu aikin yi ba.0 Response to "Rashin aikin dazanyi yasanyani ajiye digirina a gefe na kama sana'ar siyar da abinci - Inji Kyakkyawar budurwa"

Post a Comment