--
 Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan Super Eagles tallafin Miliyan biyu

Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan Super Eagles tallafin Miliyan biyu
Kaftin ɗin Tawogar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, Super Eagles, Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan ƙasar, Kingsley Obiekwu tallafin Naira Miliyan 2.

A lokutan bayan ne dai Obiekwu, wanda da shi Nijeriya ta lashe gasar'Olympic' ta 'Atalanta 96', ya baiyana cewa ya na fama da matsin rayuwa, inda motar shi kwaya ɗaya tak ya ke haya da ita domin ya kula da iyalinsa.

Tsohon ɗan wasan, wanda ya buga a Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Rangers International da ke Enugu da Udoji United, ya ce ya shiga harkar hayar mita ne sabo da matsin rayuwa.

Hakan ne ya sanya Ahmed Musa ya tausaya masa, inda ya bashi tallafin Naira Miliyan 2.

Ƴan Nijeriya da dama ne su ka riƙa godewa da yaba wa Ahmed Musa ta kafafen sadarwa.

0 Response to " Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan Super Eagles tallafin Miliyan biyu"

Post a Comment