--
Baya ta haihu: Ba gobe zanyi aure ba, CewarJaruma Aisha Tsamiya

Baya ta haihu: Ba gobe zanyi aure ba, CewarJaruma Aisha Tsamiya
Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ba a gobe Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 ba ne za a ɗaura mata aure kamar yadda aka yaɗa a soshiyal midiya.

Wannan sabuwar sanarwar ta biyo bayan yaɗa wani katin gayyatar aure ne wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ana cewa na auren jarumar ne.

A katin, an nuna cewa fitacciyar jarumar za ta yi aure a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022.

A katin, wanda mujallar Fim ta gani, an bayyana sunan sahibin nata, wato Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano.

Tun da labarin auren ya ɓulla a soshiyal midiya abokan sana’ar A’isha su ka shiga yi mata fatan alheri, inda kusan dukkan su sun ɗora hoton ta tare da katin auren.

To amma ɗazu ɗazun ban Aisha Tsamiya ta hau Instagram ta rubuta cewa, “Assalamu alaikum, jama’a barkan mu da warhaka. Na gode da addu’o’in ku da fatan alkhairi, na ji daɗi sosai, amma aure na ba 25th ga wannan watan ba ne, sai next month in-sha Allah……Na gode Allah ya saka da alkhairi.”

0 Response to "Baya ta haihu: Ba gobe zanyi aure ba, CewarJaruma Aisha Tsamiya"

Post a Comment