--
DA DUMI-DUMI:- SHUGABA BUHARI BA SHINE MATSALAR TSARON AREWA BA

DA DUMI-DUMI:- SHUGABA BUHARI BA SHINE MATSALAR TSARON AREWA BA


 SHUGABA BUHARI BA SHINE MATSALAR TSARON AREWA BA


DAGA Datti Assalafiy




Wani yace Malam Datti Assalafiy ka fada wa shugaba Muhammadu Buhari idan ba zai iya magance matsalar tsaron Arewa ba to ya ajiye mulkin


Jama'a matsalar tsaron Arewa ba daga Buhari bane, matsalar tafi karfin Buhari, babu wanda zasu iya kawo karshen matsalar tsaron Arewa sai 'yan Arewa da shugabannin su



Yau idan Gwamnonin Arewa, da Sanatocin Arewa da 'yan Majalisu na tarayya da na jihohi, da Sarakunan Arewa, da Malaman addinin Musulunci na Arewa, suka hadu sukace a dakatar da duk wani aiki a Arewa, a datse duk wata hanya da filayen jiragen sama, babu abinda zai gudana a Kasar har sai anyi abinda ya dace to Wallahi za'a samu mafita


Amma inda matsalar take shine, yau akwai Gwamnoni a Arewa wadanda suke bawa manyan barayin daji irinsu Bello Turji mafaka, suna taimakonsa da kudi da man fetur da motoci da abincin dabbobi, kuma sun hana a yake su


Anyi lokacin da Gwamnan Zamfara ya hana dukkan jami'an tsaron Nigeria yakar masu garkuwa da mutane, babu wani jami'an tsaro na Gwamnatin Nigeria da ya isa ya shiga Zamfara ya kama Kidnapper



A cikin Sarakuna ana samun masu taimakon 'yan ta'adda, babban basaraken Musulunci a Arewa ya hana a fitar da sakamakon bincike kan wadanda suke taimakon ta'addanci a Sokoto, saboda an gano wasu manyan Sarakuna da suke karkashinsa wanda suke tare da 'yan ta'adda


To kuma akan haka wai kuke cewa laifin Buhari ne duka matsalar tsaron?

Ni idan ma Buhari yana da kuskure to bai wuce hakikancewarsa akan bin matakin doka kafin ayi abinda ya dace ba, ina ganin laifin Buhari kan tsantseninsa wajen bin matakin doka, kamata yayi ya taka doka ya taka duk wani Gwamna ko Sarki da yaci amanar tsaron Nigeria



Sannan gashi nan shugaban masu yaki da barayin daji a Arewa DCP Abba Kyari an dakatar dashi daga aiki, an hanashi yakar masu cutar da Arewa, an kulla masa mummunan sharri domin a kawar dashi, da hadin bakin 'yan Arewa ake yakarsa, an kasa yakar 'yan ta'adda an dawo ana yakar mai fada da 'yan ta'adda, to wannan itace Arewan da marigayi Malam Aminu Kano yace tun asali haka suke, suna taimakon masu yakar 'yan uwan su


Makircin da aka kullawa Arewa mai girma ne da manufar a karya tattalin arzikin Arewa, a yaki addinin Musuluncin da ya ginu a Arewa sannan a hanamu neman ilmi da karatun Al-Qur'ani Maigirma, ku tuna abinda aka mana a rikicin Boko Haram


Kuma duk ranar da mukayi sake mulkin Nigeria ya shiga hannun wanda ba Musulmi ba to har Musuluncin da muke gadara dashi sai an hanamu aiwatarwa a Arewa, kamar yadda akayi yunkurin hakan a Gwamnatin Jonathan, Buharin dai da wasu ke zagi suke kushewa ya taimakemu, kuma ya bamu kariya muna addini yadda ya kamata cikin 'yanci, lokaci zai tabbatar da hakan idan ya gushe



Bance Buhari baya kuskure ko bai gaza a wasu fannoni ba, amma kokarinsa ya rinjayi gazawarsa da kuskurensa, amma tabbas Shugaba Buhari ba shine matsalar Arewa ba


Muna rokon Allah Ya saka wa shugaba Buhari da gidan Aljannah, Allah Ya yafe masa laifukansa

0 Response to "DA DUMI-DUMI:- SHUGABA BUHARI BA SHINE MATSALAR TSARON AREWA BA"

Post a Comment