--
Zafafan Kalamai Da Namiji Zai Dinga Furtawa Mace Su Idan Ya Kamu Da Ƙaunarta

Zafafan Kalamai Da Namiji Zai Dinga Furtawa Mace Su Idan Ya Kamu Da Ƙaunarta


Rashin iya kalamai masu dadi na sa maza da dama rasa ƴan matan da suke nema da aure. Duk wata mace na son jin mai sonta ya na sakar mata kalamai masu daɗi wanda suke ratsa zuciya tare da kambama su. 


Sai dai ba Kowane namiji ne yasan irin kalaman Soyayya da zai ke furtawa abar ƙaunar sa ba. Wasu kuma sun sani amma kunya da kuma sakaci sai su hanashi ya furtasu. Shiyasa a yau muka yi muku wannan rubutun domin kusan irin kalaman so da ya kamata ku dinga furtasu da abar ƙaunar ku.


Ga wasu kalaman da za ka furtawa macen daka kamu da sonta domin kara cusa mata ƙaunarka a zuciyarta.


1: Allah Ya miki kyau. Duk mace tana son taji mai kaunarta yace tana da kyau (Sai ka faɗi wajen) wannan kalmar tana sa mace taji farin ciki a ranta da kuma ƙaunar wanda ya furta mata hakan.


2: Duk shigar da kika yi yana burgeni. Kayan suna dacewa da jikinki. Ita mace ƴar kwalliya ce kuma tana yi ne domin ta birge, musamman ga wanda yake sonta. Furta mata cewa shigar da tayi mai kyau ce shima yana saka ta farin ciki.


3: Kasancewa dake na yaye mini baƙin ciki da ɓacin rai. Kina faranta mini rai. Kina sani annashuwa. Irin wannan kalaman yana sa mace taji a ranta cewa ita ta musamman ce.


4: Bamu jima da haduwa ba amma tamkar munyi shekaru da sanin juna saboda yadda kika fahimceni. Hakan zai sa mace ta ƙara son ka kuma ta ƙara sakin jikinta dakai.


5: Ba zan iya rabuwa dake ba, ba kasafai maza suke iya faɗawa mata irin wannan kalaman ba. Amma idan kana furtawa masoyiyar ka irin su za taji a ranta cewa kai na musamman ne.


6: A Kullum burina bai wuce kasancewa dake ba. Ina son ganin ranar da zaki zama tawa halak malak. Wannan kalamin zai sa taji tana son kasancewa dakai a koda yaushe


7: Kina da bambamci da sauran matan wannan zamani ta bangaren(Ambaci bangaren). Sai ka lissafa irin ɓangarorin da tafi sauran mata da yawa. Hakan zai sa ta ringa jin cewa ita ta daban ce a cikin mata


8: Bana fatan ganin ɓacin ranki. A duk sanda kika kasance a cikin ɓacin rai bana samun sukuni hankali na tashi yake yi na kasa nustuwa. Wannan zai sa tasan cewa ka damu da ita.


9: Murmushinki yana bayyana mini sa'ar da nayi wajen zaban macen aure. Dariyarki na tabbatar mini da dacen da nayi wajen haifan kyawawan ƴaƴa. Hakan ba ƙaramin kara mata sonka zai yi ba.


10: Allah Ya amsa roƙon da na yi masa na samun irin macen da na roƙe Shi kuwa. Wannan kalamin yana sa mace taji cewa tana da wasu baiwa da ba kowace mace ke da irinsu ba.


Waɗannan Kalmomin na daban ne ga duk macen da zaka furta mata su. Haka nan kuma suna da matuƙar tasiri a soyayyar da kake yi da mace. Sai dai ba kowane namiji ne yasan hakan ba, wasu kuwa sunsani amma basa yi.


Da fatan maza musamman samari za su riƙa amfani da kalaman da za su kambama masoyansu da su wajen jawo hankalin su da ƙara soyayyar junansu. Kuma wannan kalaman ba wai kawai ka furtasu a baki kaɗai ba. Yi kokarin ganin ka aikatasu ta ga soyayyar da kake mata a zahiri bayan a furuci.


0 Response to "Zafafan Kalamai Da Namiji Zai Dinga Furtawa Mace Su Idan Ya Kamu Da Ƙaunarta"

Post a Comment