--
Yanzu yanzu: Abunda ke Faruwa a Jihar Kano Daga Gidan Gwamnati Zuwa Filin Rantsar da Abba Gida Gida

Yanzu yanzu: Abunda ke Faruwa a Jihar Kano Daga Gidan Gwamnati Zuwa Filin Rantsar da Abba Gida Gida

PHOTO SOURCE: FACEBOOK

Sabon Gwamnan Kano Engineer Abba Kabir Yusif, ya ce sun karbi kundin mulkin jihar Mai dauke da bashin fiye da Biliyan dari biyu da Arba'in tare da alkawarin bincika yadda aka yi Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ciyo bashin da ma yadda aka yi da kudin.


Gwamnan jihar Kano Mai jiran rantsuwa a yau Litinin 29 05 2023 Engr. Abba Kabir Yusif, ya gabatar da jawabinsa cikin harshen turanci, inda ya godewa alummar jihar Kano bisa zabarsa tare da kyautatamasa zato.


Wakilinmu a fadar Gwamnatin Kano Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar bayan karɓar kundin mulki Tawagar Gwamna sun zarce zuwa Filin wasa na Sani Abacha stadium da ke Kofar Mata a nan Kano inda za a rantsar da su.


Majiya: Freedom Radio Kano



























Photo Source: Facebook

0 Response to "Yanzu yanzu: Abunda ke Faruwa a Jihar Kano Daga Gidan Gwamnati Zuwa Filin Rantsar da Abba Gida Gida"

Post a Comment