--
Wasu masanan na yankin kasashen Afirka na sa ganin an dakatar da gudanar da cinikayya da kudin kasar Amurka Kwanakin  baya

Wasu masanan na yankin kasashen Afirka na sa ganin an dakatar da gudanar da cinikayya da kudin kasar Amurka Kwanakin baya


Asusun ba da lamuni na IMF ya fitar da wani rahoto, wanda ke cewa a halin yanzu, farashin musayar kudi tsakanin kudaden wasu  kasashen Afirka da na Amurka na ci gaba da raguwa, lamarin da ya haifar da matsin lamba ga kasashen na yankin Afirka, a fannin ingiza hauhawar fasashin kayayyaki. 
Don gane da hakan, wasu kasashen da suka hada da Zimbabwe, da kasar Afirka ta Kudu, sun dauki matakan kara kudin ruwa domin daidaita matsalar hauhawar fasashin kayayyaki a kasashen na su.
Wasu masanan kasashen Afirka na ganin cewa, yadda kasar Amurka ta kara samar da kudade, da kara kudin ruwa, ya lahanta yanayin kasuwannin kasashen duniya.
Game da hakan, tsohon ministan harkokin sadarwa na kasar Zimbabwe Supa Mandiwanzira, ya bayyana cewa, ya kamata a nemi wata hanya ta dakatar da gudanar da cinikayya da kudin Amurka. Ya ce, hakan na nufin a adana darajar kudaden sauran kasashen duniya, domin duk wata kasa mai ’yancin kai, ba za ta cimma nasara ba, idan har tana dogara sosai kan kudin wasu kasashen na daban.

0 Response to "Wasu masanan na yankin kasashen Afirka na sa ganin an dakatar da gudanar da cinikayya da kudin kasar Amurka Kwanakin baya"

Post a Comment