--
Hukuncin Kotun Daukaka Kara: ‘Yan sanda sun bankado shirin haddasa Fitina a Jahar Kano

Hukuncin Kotun Daukaka Kara: ‘Yan sanda sun bankado shirin haddasa Fitina a Jahar Kano


Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano a yau  Litinin ta sanar da jama’a shirin wasu kungiyoyin magoya bayan jam’iyyar siyasa na haddasa rikici a jihar.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kungiyoyin sun shirya fitowa kan titi domin nuna rashin amincewarsu da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan zaben gwamna a jihar.

 Sai dai ya ce rundunar ta dauki matakan tsaro da suka dace domin hana tashe-tashen hankula da ka iya haifar da karya doka da oda.

“A kan haka ne rundunar ‘yan sandan ta yi wannan gargadi ga mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan domin duk wanda ke da niyyar gudanar da wata zanga-zanga ko jerin gwano ya yi hakan ne bisa tanadin doka,” in ji Kiyawa.

 Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Usaini Gumel, ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani nau’i na haramtacciyar taro, ko zanga-zanga ko jerin gwano da ka iya jawo tashin hankali.

 Kakakin ya ce an tura jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa wasu muhimman wurare domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.

 “Duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar za a kama shi kuma a hukunta shi ya fuskanci fushin doka,” ya kara da cewa, ya kuma bukaci mazauna yankin da su kai rahoton duk wani motsi, mutane ko kaya ga jami’an tsaro domin mayar da martani cikin gaggawa. 

0 Response to "Hukuncin Kotun Daukaka Kara: ‘Yan sanda sun bankado shirin haddasa Fitina a Jahar Kano"

Post a Comment