Yanzu yanzu Anbude Shafin Cike Tallafin Karatu: Scholarship 2025 Kano State Postgraduate
Yanzu yanzu Anbude Shafin Cike Tallafin Karatu: Scholarship 2025 Kano State Postgraduate
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf tana gayyatar dalibai masu basira da kwazo don neman guraben karatun digirin gaba da digiri na biyu (Postgraduate) a shekarar 2024/2025.
Wannan shirin tallafin karatu na matakin biyu yana nufin bayar da dama ga matasan Kano don samun ilimi mai zurfi da ci gaba a fagen karatunsu.
An kaddamar da wannan shiri a shekarar 2023, inda aka dauki dalibai 550 don yin digiri na biyu a jami'o'i a kasashen India da Uganda.
A wannan karo, gwamnatin jihar ta sake bude kofa don dalibai masu sha'awar wannan dama mai amfani su nemi tallafi.
Sharuddan Cancanta:
Don samun wannan tallafin karatu, dole ne mai nema ya:
1. Kasance cikakken dan asalin Jihar Kano.
2. Ya mallaki digiri na farko mai daraja ta farko(First-Class Honours) ko makamancinsa daga kwaleji ko jami'a mai daraja.
3. Ya kasance karkashin shekaru 30 idan digirin da ya yi ya dauki shekaru hudu zuwa biyar, ko karkashin shekaru 35 idan ya dauki sama da haka.
4. Ya gabatar da takardar shaidar lafiyar jiki daga asibiti.
5. Ya kasance ya kammala NYSC ko ya gabatar da takardar kebewa (exemption) ko takardar tsallakewa (exclusion).
6. Ba ya karbar wata tallafin karatu ko tallafi na cikakken kudi a halin yanzu.
7. Ya rubuta bayanin kansa mai tsawon kalmomi
500.
8. Ya amince da ka'idojin shirin tallafin idan an zabe shi.
Ana bayar da fifiko ga wadanda ke da nakasa ko kuma wadanda suke neman karatun da zai cike gibin ayyukan jihar.
Takardun da Ake Bukata:
1. Takardar haihuwa
2. Shaidar asali daga Kano
3. Shaidar firamare
4. Shaidar WASC/GCE/SSCE/NABTEB/NBAIS
5. Takardar digiri
4. Shaidar WASC/GCE/SSCE/NABTEB/NBAIS
5. Takardar digiri
6. Kundin sakamakon karatu (Academic transcript)
7. Takardar lafiyar jiki
Yadda Za a Aiwatar:
1. Je zuwa gidan yanar gizon:
(http://scholarship.kanostate.info)don cikewa.
2. Buga fom din da aka cike tare da hada dukkan takardu, sannan ka mika su a adreshin: Conference Hall, Kano State Scholarships Board, No. 23 Abdullahi Bayero Way, Kano.
Albahirinku: Ina Masu sana'anar Siyar da Data Ko Siyan Data ta Amfani Yaufa sullum???
Wannan Shafin mun Samar Muku da Website da Application Wanda Zaku sayi Data a Farashi Mai Rahusa.
Ga Yadda Farashin Datarmu Yake:
0 Response to "Yanzu yanzu Anbude Shafin Cike Tallafin Karatu: Scholarship 2025 Kano State Postgraduate"
Post a Comment